Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Sadarwa ta Najeriya da ta tattara bayanan wayoyin jama’ar kasar cikin watanni uku.
Umarnin na shugaba Buhari ga NCC na kunshe ne a cikin Dokar Tantacewa ta Kasa da Aka Bude don Rajistar Katin SIM.
A cewar Buharin Umarnin za’a aiwatar dashi gabaɗaya a ƙarshen Yuli 2021.
Manufar ta bayyana cewa aiwatar da Kundin Tsarin Bayanan Kayan Kasuwanci za’ayiwa duk wayoyin hannu masu rajista da masu irin waɗannan na’urorin.
Hakan na cikin kokarin gwamnati wanda ya kunshi Rijistar Katin SIM don cimma tsaro daga tsarin digital.
Haka nan lambar ta IMEI na bada rahoton cewa ko an sace wayar ko kuma duk wani abu da aka aikata da ita ta hanyar DMS ta inda za’a dakatar da wayar daga aiki koda an saka SIM ko wane iri a ciki.
Haka nan DMS zai bada dama ga duk masu kafafen sadarwar aiki akai da kuma duba lambar IMEIs kafin su bar layin ya fara aiki a kan hanyar sadarwar su.
Bugu da kari, za a samar da kwararrun masu wayar hannu don duba lambobin wayar da sukayi rigista.
Hakan na cikin kudurin gwamnatin na daukar dukkanin rahotannin waya da lambobinsu koda an sace kuma koda an saka wani layin wayar.