
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da basaraken kasar Morocca sarki Mohammed na V1 a game da shirin hada ka na bijiro da ayyukan ci gaba tsakanin kasashen biyu, ciki hade da batun samar da iskar gas da kuma sarrafa taki.
Shuwagabannin biyu sun nuna jajircewar yiyuwar hakan tare da cewa za’a fara ayyukan cikin kankanin lokaci.
Hakan yana kunshe ne cikin sanarwa da mashawarcin shugban kasar na musamman a harkan yada labarai Garba shehu ya fitar ranar 1 ga watan fabrairun 2021.
Shugaba Buhari yayi marhaba da kyakkyawar alakar Najeriya da kasar na Morocco tun bayan ziyarar da basaraken ya kawo Najeriya a shekarar 2016 yayin da Buharin ya ziyarci kasar a 2018.
Ya kuma godewa mai martaba sarki Muhammad bisa goyon bayan dayake bayarwa wajen yakar ta’adanci da tsatsaurar ra’ayi.
Ya kuma godewa masarautar bisa goyon bayanta a harkar ilimi ta hanyar daukar nauyin karatu kyauta da kuma horaswa.
