
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na ganin ta kare yan Najeriya daga cutar Coronavirus.
Shugaban ya bayyana haka a sakon san a sabuwar shekara da aka watsa a Abuja.
shugaban ya ce Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shirye domin raba allurar rigakafin COVID-19 ga yan kasa.

Ya kuma umarci ‘yan Najeriya da su kiyaye da kaidojin da aka dingaya na kariya daga kamuwa da cutar COVID-19 .
yake jawabi akan yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatinsa, Buhari ya baiyana cewa gwamnatin ta samu nasarori masu yawa zuwa yanzu kuma a wannan shekarar, gwamnatin za ta kara himma domin cigaba da yakar cin hanci da rashawa a kasar .
Shugaban Yace za a cimma hakan ne ta hanyar hadin gwiwa da dukkanin bangarorin gwamnati domin ganin an kau da nau’i na ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.
Shugaban ya kuma bayyana shirin cigaba da aiki tare da majalisar dokoki domin samar da dokokin da za su karfafa yaki da cin hanci da rashawa.
