Shugaban Buhari, Ya Baiwa Tsoffin Masu Yiwa Kasa Hidiman 110 Aiki Da Kuma Tallafin karatu .

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya baiwa tsoffin ‘masu yiwa kasa hidiman 110 aiki a Gwamnatin Tarayya da kuma ba su gurbin karo ilimi domin karatun digiri na biyu har zuwa digiri na uku a kowace jami’a a Nijeriya.

Da yake jawabi a wajen bikin karrama yan bautar kasa na shekarar 2018/2019 wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Kasa, a Abuja, Shugaba Buhari, ya kuma sanar da kyautar kudi ga mambobin bautar kasar .

Shugaban Buhari Ya umarci hukumomin gwamnati da su tabbatar sun aiwatar da duk wani abubuwan da suka dace ga wadanda suka samu kyautar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun maitaimaki na musanman ga shugaban kasa akan harkokin yada labarai Femi Adesina.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa yiwa kasa hidima ta kasance wani ginshiki na hadin kan kasa ta hanyar nuna a al’adu daban daban .

Shugaba Buhari ya yaba wa matasan Najeriya masu yi wa kasa Hidima saboda kasancewa a sahun gaba a yakin da ake yi da cutar COVID-19.

Da yake yaba wa Ma’aikatar Matasa da Raya Wasanni ta Tarayya Shugaban Buhari ya bukace su da su cigaba da gudanar da ayyukansu yanda ya kamata.

Sannan ya bukaci matasan Najeriya da su guji duk wasu munanan halaye da zai kawo koma baya ga tattalin arziki da zamantakewar al’umma da cigaban kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply