
Shugaba Buhari zai yi jawabi ga majalisun tarayya a ranar alhamis.
Mai taimakawa shugaban kan kafofin yada labarai Lauretta Onochie ne ta bayyana haka ta kafar sada zumunta na twitter a ranar litinin.
Gidan radio dandal kura ta rawaito cewa kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabaimila ya tabbatar da amincewar shugaba Buhari na yin jawabi ga majalisaun kan karuwar matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan kudirin da aka mika kan kisan da akayiwa manoma a jihar Borno.
