Shugaba Buhari Zai Tattauna Da Gwamnonin Jihohi 36 Akan Matsalar Farashin Man Fetur A Ranar Alhamis.

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tattauna tare da gwamnonin jihohi 36 kan matsalar farashin man fetur a ranar Alhamis.

Ministan kwadago da samar da ayyuka sanata Chris Ngige shi ya bayyana haka bayan taron da gwamntin tarayya da kungiyar kwadago suka gudanar.

Yayin da yake bayani ga manema labarai kan sakamakon taron, ministan yace kungiyar kwadago ta bincike rahoton kwamiti kan fasalin farashin man kamar yadda aka amince a taron da ta gabata kuma sun gabatar da rahoton tare da kamfanin man fetur ta kasa.

Ministan ya kara dacewa gwamnatin tarayya ta gama tattaunawa tare da kungiyar kwadagon kan farashin man.

Yayin da yake magana kan kudin wutar lantarki, ministan ya bayyana cewa kwamiti kan kudin wutar lantarkin tayi gyare gyare kuma maida kwamitin na aiwatarwa damin aiwatar da ayyukan da suka hada da mitan wuta.

Ya kara dacewa mambobin kwamitin tare da ministan wutar lantarki zai tabbatar da DISCOS ta sanya mita ga jama’a saboda akwai rahoton da ke cewa basa son raba su sunfi son suna bada takardan bill.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustafa ya yabawa kungiyar kwadagon bisa kokarin su a lokacin da ake tsaka da matsalar tattalin arziki. wanda aka yabawa Najeriya da fitar ta daga koma bayan tattalin arziki a sashe na 3 a shekarar 2020.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply