
Shugaba Buhari yayi gargadi cewa za’ayi hukunci mai tsanani kan duk wani kanfanin wutar lantarki ko wakilan kanfanin wutar lantarki da suke siyar da mita ga kostomomin su.
Shugaban yace zai sanya hukunci mai tsanani kan duk wani kanfanin rarraba wutar lantarki ko wakilan su da suke siyar da mitan wutar lantarki ga kostomomin su bayan umurnin da akayi musu na rabawa kyauta.
Wannan ya fito ne ta hannun mashawarci na musamman ga shugaban Buhari kan kayayyaki Ahmed Rufai Zakar wanda ya wakilci shugaban a taron kwamiti na masu ruwa da tsaki kan jadawalin kudin wutar lantarki a Ibadan.

Yace shugaban ya fahimci matsalar yan Najeriya day a shafe su game da wutar lantarkin kuma yana kokarin magance gurbatattun ciki.
Shugaban yace tuni ya bada umurnin rarraba mita miliyan 6 ga masu anfani dasu domin dakatar da wasu kan kiyasta kudin bill ko kara shi.
