Shugaba Buhari Yayi Gargadi Ga Hukumomin Gwamnati Da Su Kara Kaimi Wajen Samar Da Kudaden Shiga.

BUHARI LARGE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari yayi gargadi mai tsauri ga hukumomin gwamnati da su kara kaimi wajen samar da kudaden shiga domin cimma burin su.
Hakkan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban kasa a bangaren yada labarai da hulda da jama’a Mallam Garba Shehu ya bayar.
Shugaban kasar yayi wannan gargadi ne bayan ya sanya hannu a kan takadar kasafin kudirin kasa naira trilliyan goma sha uku da digo hamsin da chasa’in da takwas na shekarrar 2021 tare da takadar kudi na shekarar badi a ranar alhamiis.

Wakilyar mu Aisha Sale ta bayyana cewa hukumomin da shugaban yayi kira gare su sun hada da hukumar tace man fetur ta kasa, hukumar jirajen ruwa ta kasa ,hukumar kudaden shiga ta kasa,humar fice da shige ta kasa,hukmar fasakaure da sauran hukumomin.

Shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa da cewa duk da rikice-rikicen da cutar corona virus ta haifar, an samu an aiwatar da kasafin kudi na shekarrar 2020 ta hanyar da aka saba.

Shugaban ya yaba wa majalisar dokoki kan kammala aikin

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply