Shugaba Buhari yayi Gargadi AKan Zanga Zanga A Kasar nan.

buhari in borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A ranar litinin ne shugaba Buhari yayi gargadi akan sake maimaita tarzomar zanga zanga a fadin kasar nan.

Shugaban ya bayyana haka yayin bude babban taron shekara shekara na shuwagabannin sojojin kasa.

Shugaban yayi gargadin cewa za a yi maganin duk wani aikin ta’adi da ake fakewa da doka ko zanga zangar lumana domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba a kasar nan.

Ya bayyana manufar gwamnati na kare yan kasar ta wajen gudanar da zanga zangar lumanakamar yadda doka ta kasa ta kafa, idan za a iya tunawa zanga zangar ENDSARS an shirya ne domin lalata dukiyoyi da rayukan al’umma.

Haka kuma ya yabawa dakarun sojojin Najeriya na kokarin su wajen daidaita doka a jihohi da dama a kasar nan yayin zanga zangar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply