Najeriya: Shugaba Buhari Yayi Bayani Kan Harbin Da Akayi Fadar Shugaban Kasar

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni ayi binciken abinda ya faru alhamis din data gabata yayin da akaji harbin bindiga a fadar shugaban kasar.

Malam Garba Shehu mataimaki na musamman kan sha’anin yada labarai da hulda da jama’a na shugaban kasar ne ya fitar da rahoton inda yace abun ba’a cikin fadar shugaban kasar ya faru ba kuma shugaban kasar baya cikin hatsari.
Ya kara da cewa shugaban kasar ya bari ayi bincike kuma zai bar shari’a ta dauki mataki.

Rahoton ya bayyana rashin dadin yadda yan adawa ke canza maganar inda suke cewa gwamnatin aka kaiwa harin.

Ya kuma jaddawa cewa abun ya faru a waje ba cikin gidan shugaban kasar ba kuma masu kula da fadar shugaban kasar nada kwarewa musamman ta hanyar rike makamai kuma sun san dokar rike makaman.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply