Shugaba kasar Najeriya Muhammadu Buhari yace Najeriya zata tallafa wajen daidaita kasar Chadi da kuma komarta kan tsarin mulkin demokardiyya.
Hakan yana kunshe a cikin sbayani da mai Magana da yawun shugaban Mr Femi yayi jumma’a yayin da shugaba Buhari ya karbi ziyarar Lt.-Gen. Mahamat Idriss Deby, da ga marigayi Idriss Deby daya cigaba da shugabanci bayan rasuwar mahaifin nasa a 19 na afrilu daya gabata na wannan shekara.
Cikin watanni 18 masu zuwa ne ake sa ran demokaradiyya zai daidaita a kasar na hadi wanda shugaban Buhari yace Najeriya zata tallafa wajen tabbatar da hakan.
Shugaba Buhari yace hakika kasar Najeriya da chadi nada alakar al’adu, muhalli daa sauran su wanda hakan zai taimakwa kasashen 2 kuma yace Najeriya tana sane da rawar da kasar tayi na taimakwa a yakar ta’addanci inda yace hadin kan zataci gaba da daurewa.
Haka kuma ya misalta irin dangantaka tsakanin sa da marigayi Idriss Deby da cewa aboki ne musamman dama wa kasar Najeriya inda yake sahun gaba-gaba wajen kare Najeriya tare da cewa a ko yaushe kofa a bude yake ga gwamnatin chadi idan bukatan hakan ta taso.
Kuma yace Najeriya zata karfafa yankin tapkin chadi da ma rundunar tsaro na hadin gwiwan.
Shugaban kasar na Chadi Janar Muhammat Idris Deby ya godewa Najeriya da irin kulawarta yayin rasuwr mahaifin sa kuma ya bayyana Muradin gwamnatin su da suka hada da tsaro da hadin kai a kasar Chadin
Yace Najeriya tana alaka da kasar Chadi a bangarori da dama kuma yay aba da irin abota tsakanin kasashen inda yaba da tabbacin yin adalci a zaben da za’ayi cikin wtanni 8 masu zuwa.
NAN ta ruwaito cewa tuni Mahamat Deby ya wuce filin jrigin sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja zuwa brinin Ndjamena.