Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Da Yan Fashi Suka Kai Makaranta A Jihar Katsina.

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da yan fashi da makami suka kai makarantar sakandaren kimiyya na gwamnati dake Kankara a jihar Katsina inda yayi kira ga rundunar sojoji day an sanda dassu tabbata babsu wani dalibin daya jikkata ko ya bata.

Shugaban yayi kira ga hukumar makarantar da ta duba dukkan bayanan daliban domin harbe harben da akayi ya sanya da dama tserewa ta Katanga.

Haka kuma an bukaci iyayen da suka je suka dauki yaran su das u sanarwa hukumar makarantar da yan sanda domin sanin adadin daliban.

Yayi addu’a ga iyalan daliban da hukumar makarantar da ma wadanda suka jikkata haka kuma ya bukaci da a cigaba da bada goyon baya ga jami’an tsaro domin fatattakar yan ta’adda day an fashi da makami.

A wani labari da shugaba Buhari ya samu daga gwamna Aminu Bello Masari da kuma babban hafsan rundunar sojoji laftanar janar TY Buratai rundunar sojoji da taimakon sojojin sam sun gano mabuyar yan fashin kusa da dajin Zango Paula a Kankara kuma tuni aka kai musu hari.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply