
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa gwamnatin sa bazata lamuncewa wani kabilu ko kungiyoyin addini su haddasa tashin hankali ko tsana tsakanin al’umma ba.
Yayi alkawarin cewa gwamnatin sa zata kare dukkan addinai da kabilu manya ko kanana kamar yadda kundin tsarin kasa ta tanadar.
Hakan yana kunshe cikin sanarwa da mashawarcin shugaban kasan kan harkokin yada labaran Garba Shehu ya fitar a game da batun tashin hankali a wasu bangarorin kasar.

Sanarwar na kunshe da cewa shugaba Buhari yayi ala wadai da tashin hankalin kuma yaba da tabbacin cewa gwamnatin sa zatayi aiki tukuru domin dakile bazuwar iren-iren tashin hankali nan kasa.
Ya roki shuwagabannin addinai tare da gwamnoni da zababbun shuwagabanni dasu hada kai da gwamnatin tarayya domin tabbatar da cewa ba’a raba hankulan jama’a a yankunan suba.
