Shugaba Buhari Yace Ba Za A Samu Wani Cigaba Mai Dorewa Idan Har Babu Isassun Kayakin Aiki.

BUHARI FEC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari yace babu wani cigaba mai dorewa idan har kasa bata da isassun kayakin aiki.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bada shawara na musamman ga shugaba Buhari kan kafar sadarwa Femi Adesina ya fitar.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan yayin da yake karban bakwancin Wang Yi kuma ministan harkokin kasashen waje na kasar Sin.
Shugaba Buhari yayi godiya ga kasar Sin da irin taimakon su ga kasar nan a bangarorida dama kamar su ginin jirgin kasa, tituna da sauran su.

Mr. Wang Yi ya yaba da kyakkyawar alakar dake tsakanin shugaba Buhari da kuma shugaba Xi Jinping na kasar Sin,
Yace kasar Sin tana son fara aikin diplomasiyya a Afrika kuma an zabi kasar nan a matsayin na farko a shekarar 2021.

Mr. Yi yace kasar sa zata goyi bayan kanfanonin yan kasar domin kara zuba hannun jari a Najeriya haka kuma kasar zata taimaka da fasahar ta a wasu bangarorin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply