Shugaba Buhari Yaba Da Umarni Da A Kawo Karshen Yan Fashi A Jihar Zamfara.

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari yayi umurnin gaggawa kan yawan harin yan fashi a jihar Zamfara.
Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban na musamman kan yada labarai Mallan Garba Shehu ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya bada umurni ga babban mai bada shawara kan harkokin tsaro ta kasa manjo janar Babagana Monguno cewa ya kamata a kawo karshen harkokin yan fashin da yayi sanadiyyar rayukan mutane da dama da sanya wasu da dama rasa matsugunan su.

Idan za a iya tunawa dai kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Nasir Magarya ya rubuta wasika ga shugaba Buhari inda ya bukaci shi da ya kawo karshen kashe kashen da akeyi a jihar.

Da haka ya sanya wani taro da za a gudanar da zai maida hankali kan matsalolin tsaro, rashawa da hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba wanda yake ta’azzara rikicin a jihar.

Taron zai samu halartar manjo janar Bashir Magashi mai ritaya, Ogbeni Ra’uf Aregbesola, Arch. Olamilekan Adegbite, ministan tsaro, ministan harkokin cikin gida, ministan ma’adanai darakta janar na hukumar tsaron farin kaya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply