Shugaba Buhari Ya Zabi Audi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar NSCDC

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da zaben Dr Ahmed Audi a matsayin sabon komanda janar na hukumar tsaron farin hula na kasa NSCDC.

Haka zalika shugaba Buhari ya zabi Haliru Nababa a matsayin sabon akwanta janar na hukumar kaso karkashin sabon dokar hukumar na shekarar 2019.

Cikin sanarwar da daraktan labaru da hulda da jama’a na hukumar cikin gida Mohammed Manga ya fitar, yace Muhammad Audi ya kasance mafi dacewa da maye gurbin komanda janar na hukumar mai barin gado.

Minista Rauf Aregbesola, ya taya sabbin wadanda aka zaban murna kuma yayi musu kira dasu tabbatar sunyi aiki da tsarin hukumar su.

Ya kuma bukace su dasu tabbata akwai hadin kai da sauran jami’an tsaro a kasar domin bada tsaro yadda ya dace da daukaka darajar yan Najeriya da ma yan ketere wadanda suka amince da shugabancin shugaba Buhari.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply