
From :Rakiya Garba Karaye, Maiduguri
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohuwar Ministar kudi da ttatalin arziki Dr Ngozi Okonjo-Iweala murnar zabenta da akayi a matsayin Darakta Janaral ta kungiyar kasuwanci ta duniya wato World Trade Organisation.
Shugaban yace yana mata fatan alkhairi dashi da gwamnatinsa dama dukkanin yan Najeriya inda yace abun murna ne da kuma girma da kasar ta samu.
Haka nan yace Iweala wadda tayi makaranta a Harvard kuma sananniya ta fanni tsumi d tanadi ta samu wan nan matsayin inda zata bautawa duniya da al’umma kuma ya bayyana cewa tana da tarihi mai kyau na gaskiya, jajircewa da son aikinta wanda hakan zai kawo cigaban al’umma.

Shugaba Buhari ya kuma tabbatar cewa Dr Okonjo-Iweala wadda shekaru da dama take da tarihi mai kyau ta hanyar gyaran hanyoyin tsumi da tanadi wadda ta rike mukamin ministar kudi inda daga baya ta koma ministar kasashen waje zatayi ammfani da damar ta wajen cigaba da karfafa kungiyar inda kowa zai amfana.
