Shugaba Buhari ya Taya Biden Da Haris Murnar Zama Shugabannin Amurka

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Rakiya Garba Karaye, Maiduguri
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasar Amurka Joe Biden zama shugaban kasa da Sanata Kamala Harris a matsayin mataimakiyar sa.

Ya bayyana cewa yana fatan a samu hadin kai da taimakon Najeriya da kasar Afrika baki daya.

Hakan na cikin rahoton da mataimakin shugaban kasar na musamman kan harkar yada labarai da hulda da jama’a Malam Garba Shehu ya fitar wanda Rakiya Garba Karaye ta hada mana rahoton.

Shugaba Buharin yace yana daukin ganin mulkin shugabancin Biden inda yake fatan hakan zai karfafa tsakaninsu da ayyuka tare wajen dakile ta’addanci, canjin yanayi, yaki da talauci da karfafa tattalin arziki da fadada cinikayya.

Haka nan shugaban kasar ya bayyana cewa yana ganin zai sa a samu cigaba a wuce lokacin da akwai kyakkyawar alaka tsakanin kasashen 2.

San nan rahoton ya bayyana cewa shugaba Buhari da dukkanin yan Najeriya na taya shugaba Joe Biden murna da kuma jin dadin bawa mace ta farko kuma yar asalin Afrika da Asia matsayin mataimakiya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply