
By:Babagana Bukar Wakil, Maiduguri.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soke dukannin shuwagabannin tsaro tare da nada sabin shuwagabanin tsaro.
Mataimakin shugaban kasa a bangaren yada labarai Mr. Femi Adesina shine ya bayyana hakkan a wata sanarwa a jiya.
Gidan Radiyo Dandal Kura Radio International sun bayyana cewa Major-General Lucky Irabor, zai maye gurbin General Abayomi Olonisakin a matsayin hafsan tsaro sai kuma Manjor-janaral Ibrahim Attahiru zai maye gurbin Laftanar Janaral Tukur Yusuf Buratai a matsayin hafsan sojojin kasa .

inda Rear Admiral A.Z Gambo zai maye gurbin Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin hafsan sojojin ruwa sai kuma Air-Vice Marshal I.O Amao, zai maye gurbin Air Marshal Sadique Abubakar a matsayin hafsan sojojin sama.
Dukkanin tsofin shuwagabanin sunyi aiki na shekaru biyar da wata shida tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada su a ranar sha bakwai da watan July shekarar 2015. Shugaba Buhari ya taya sabbin shuwaganin murya.
