Shugaba Buhari ya nemi goyon bayan shuwagabannin addinai a yakar ta’addanci, da annobar COVID-19

shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yyi kira ga dukkan shuwagabannin addinai a fadin kasar da su hada kai a tare a shawo matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane, yan bindiga da kuma annobar Coronavirus.

Hakan yana kunshi cikin sanarwa da mai Magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya rattaba hannu bayan amsa gaisuwar bikin sallar ga sarkin musulmi mai martaba Sa’ad Abubakar na lll
Haka zalika shugaban Buharin yayi kiran tataunawa tsakanin shuwagabannin addinai biyu masu karfi a Najeriya duk domin samun zaman lafiyar Najeriya
Ya kuma yabawa sarkin Musulmi da irin kyakyyawan shugabanci al’umman musulmi da irin hadin kai da aka samu a karkashin

Haka zalika sarkin musulmin yaba da tabbacin bada gudumawar sa wajen hadin kan kasa kuma yaba da tabbacin goyon bayan sa wajen magance matsalolin kasar.