Shugaba Buhari Ya Mika Sakon Ta’aziya Ga Iyalai Sheikh Ahmed Lemu

BUHARI THUMB
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa najeriya Muhammadu Buhari ya kwatanta marigayi Sheikh Ahmed Lemu da cewa hakika za’ayi rashin masanin addini, mashar’anci, malami da kuma marabuci.

Yar marigayin Maryam Lemu ne ta kafa a shafin ta na Facebook cewa Sheikh Lemu ya rasu a safiyar Alhamis a birnin Minna na jihar Niger.

Marigayi Lemu ya kasance shugaban kwamitin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a shekarar 2011 don duba rikicin siyasa daya abku a baya na wancen lokaci, kuma shine daya daga cikin yan najeriya biyu da sukaci shaidar yabon kasan waje na sarki Faisal International Award.

Shugaban kasa Buhari yace, marigayi Lemu yana daga cikin malaman addini da suke amfani da basira wajen yada ilimi ta yadda suke karantar da islama ta hanya mafi fahimta.

Shugaban kasar ya kuma yi addu’ar Allah Ubangiji Ya basa ladan hidima da yayi wa musulunci da kuma fahimtarwa daya bayar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply