Shugaba Buhari Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro.

buhari-talkingsmall
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da sabbin hafsoshin tsaro.

inda ya bukace su da su kasance masu kishin kasar su yayin gudanar da ayyuka.

Shugaban ya taya su murna yayin da suka kama aiki, ya kara dacewa gwamnatin sa tayi alkawarin kare kasar ta da farfado da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Haka kuma yayi kira a gare su da su mutunta sauran jami’an su kuma yace gwamnati zatayi iya kokarin ta wajen samar da kayakin aiki a sauran kayakin bukata.

Wadanda suka halarci taron akwai manjo janar Leo Irabor babban hafsan tsaro, manjo janar I Attahiru babban hafsan sojojin kasa, Rear Admiral AZ Gambo babban hafsan sojojin ruwa sai kuma Air Vice Marshal IO Amao babban hafsan sojojin sama, wanda ministan tsaro manjo janar Bashir Magashi mai ritaya ya jagoranta.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply