Shugaba Buhari Ya Gana Da Gomna Masari

BUHARI FEC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari a ranar litinin ya samu cikakken bayani a garin Daura na jihar Kasina kan garkuwa da yaran makarantar gwamnati na Government Science Secondary School dake karamar hukumar Kankara .

inda gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari ya basa cikakken bayanin cewa ana kokari fito dasu cikin koshin lafiya.

Hakan yana kunshe cikin sanarwa da mataimakin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar a ranar on 14 ga watan disamba 2020

Gwamna masari bayan tattaunawa da shugaban kasa na sa’a daya ya bayyana wa manema labarai cewa an samu cigaban kuma ana hangen nasara kuma yace tuni hukumomin tsaro sun gano inda yaran makarantar suke

Haka mataimakin gwamnan jihar Manir Yakubu, yace an yi Magana da yan garkuwa kuma tuni anfara tattaunawa game da kokarin dawowan su gida lafiya

Gwamna ya kuma ce shugaban kasa a shirye yake game da ceton yaran makarantan tare da cewa dacewar sanar wa da shugaban kasan halin da ake ciki yana da muhimmanci kwarai

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply