Shugaba Buhari Ya Bukaci Matasa Da A Dama Dasu A Siyasa

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hakika nasarar jam’iyyar APC ta dangane da karfafa shugabancin demokradiyya na cikin gida, hade da zabe mai sahihanci da inganta bukatu da tsare-tsaren al’umma

Yayin taron da shugaban yayi tare da matasa magoya bayan jam’iyyar ta yana, shugaba Buhari ya bayyana cewa rajistarv jam’iyya da ake kanyi tamkar shirin cigaba ne a bai daya, ikon mallaka da kuma tabbatar da an dama da matasan.

Yace ya isa mahaifar san a garin Daura ne sake sabonta kasancewar mamba a jam’iyyar na APC

Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatin tarayya zata cigaba da bullo musu da tsare-tsare na ci gaba tare da hada musu kwamitin da zai kulla da ayyukan matasa zalla. Ya kuma bukace su da shiga jam’iyyar ta APC sannan ya gode musu da kasancewa tare da jam’iyyar tsawon shekaru.

Cikin jawabin sa, wakilin matsan na kasa Barrister Ismaeel Buba Ahmed, ya godewa shugaba Buhari da irin dauki daya saba kaiwa matasan a lokuta da ake bukata a fadin jihar wadanda suka hada da tsarin matasa na N-Power, asusun kudi na naira biliyan 75 tare da tallafa wa sana’o’in matasa musamman domin rage radadin COVID-19.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply