Shugaba Buhari Ya Bayyana Cewa Zai Baiwa Niger Goyon Baya A Zaben Da Zasu Gudanar

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan zata baiwa jamuhuriyar Nijar cikakken goyon baya, yayin da za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a watan nan.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bada shawara na musamman kan yada labarai ga shugaba Buhari, Femin Adesina ya fitar a jiya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a fadar shugaban kasa yayin daya karbi bakwancin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo wanda ya jagoranci tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen afrika ta yamma.

Ya yabawa shugaba Mahamadou Issoufou da bai sanya kan sa cikin tsarin mulkin kasar sa ba wanda ya ajiye shi kan karagar mulki.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya bayyana cewa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen afrika ta yamma zata tabbatar an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci a jamhuriyar Nijar duk da yanayin tsaro da ake ciki.

ya kara da cewa ana gudanar da taro tare da masu ruwa da tsaki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply