Shugaba Buhari Ya Bayyana cewa za a bude Iyakokin kasa Nan Bada Jimawaba.

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya baiyanawa gwamnoni na jihohi 36 cewa Gwamnatin Tarayya na neman sake bude kan iyakokin kasashen nan bada jimawaba .

Shugaba Buhari, wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da gwamnonin jihohin kan batun tsaro, ya bukace su da su yi aiki tare da sarakunan gargajiya da membobin al’umma domin samun bayanan sirri wanda zai taimaka wa ayyukan hukumomin tsaro.

Shugaban, wanda ya saurari jawaban kowane gwamna akan matsalolin tsaro ya baiyana cewa a cikin al’ummomin akawi mutane da da zasu iya ba bayanan ga hukuma.

Da yake bayani kan yanayin tsaro a kowane yanki, Shugaban ya ce gwamnatinsa ta yi rawar gani a Arewa maso Gabas da Kudancin Kudu, yana mai cewa halin da Kudu maso Kudu ke ciki har yanzu abin damuwa ne.

Ya bayyana cewa rufe iyakokin kasa wani bangare ne na kokarin hana shigo da makamai da kwayoyi cikin kasar .

Shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa sojojin kasar zasu cigaba da samun goyon bayan da suke bukata domin yakar masu aikata laifuka.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply