Shugaba Buhari Ya Bayyana Cewa Nijeriya zata Fara Amfani Da Dimbin Arzikin Iskar Gas Da Take Da Shi.

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

SHUGABA kasa Muhammadu Buhari ya baiyana cewa kasar zata fara amfani da dimbin arzikin iskar gas da take da shi.

Shugaban ya Baiyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da cibiyar iskar Gas dake garin Oredo a jihar Edo.

shugaban yace kamfanin kula da man fetur na Najeriya zai kula da cibiyar.

Haka zalika Yace, cibiyar za ta dinga cire gangar iskar gas A kullum wanda yake kimanin naira miliyan 205 a kowace rana zuwa kasuwar cikin gida.

Shugaban yace aikin na daya daga cikin kudirin gwamnatin sa na bin diddigin da kokarin samar da iskar Gas a Najeriya a shekarar 2020.

Tun da farko, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ya baiyana cewa aikin akwai jajircewar kamfanin NNPC na samar da da iskar gas tare da kara darajar iskar gas a nigeriya .

A cewarsa, dukkanin Man Fetur da Gas a na tacesu ne a kasuwar Najeriya.
Manajan Daraktan rukunin kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce shugaban kasar ya ba da umarnin ga Maaikatar Albarkatun Man Fetur da NNPC.

Kyari ya ce an tsara wurin, an gina shi kuma an kawo shi ta hanyar amfani da abubuwan da ke cikin Najeriya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply