Shugaba Buhari Da Mataimakin Sa Sun Karbi Rigakafin Cutar Corona.

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari tare da mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo sun karbi rigakafin cutar Corona.

Dr. Suhayb Sanusi ne yayiwa shugaban kasa rigakafin a ranar asabar da misalin karfe 11 da minti 51 na safe bayan wani taro tare da mukarraban gwamnati a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Haka kuma anyiwa mataimakin sa Osinbajo wanda likitan sa Nicholas Audifferen yayiwa da misalin karfe 11 da minti 57 na safe.

Shugaba Buhari tare da mataimakin sa suna cikin wadanda aka fara yiwa rigakafin a fadin kasar nan bayan wasu ma’aikatan jinya da akayi musu a babban asibiti dake Abuja.

Tuni dai hukumar dake kula da ingancin abinci da magunguna ta amince da rigakafin sama da miliyan 3 wanda ya shigo kasar Najeriya a ranar Talata 2 ga watan Fabrairun wannan shekara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply