Shugaba Buhar Ya Isa Maiduguri A yau

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa sansanin sojin sama dake Maiduguri jihar Borno tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Shugaba Buhari ya sauka ne da misalin karfe 11:15., cikin tsauraran matakan tsaro.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da ‘yan majalisar wakilai ta kasa da na jiha, Sanata Ali Modu Sheriff, Sanata Kashim Shetima da dai sauran su.

Shugaban ya samu rakiyar Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da wasu manyan jami’an gwamnati.

Shugaba Buhari ya kuma kaddamar da Air Craft Hanger na Oriental Energy Resources Limited mallakin Alhaji Muhammed Indimi a filin jirgin saman Maiduguri.

Shugaban ya kuma kaddamar da gadar sama mai nisan kilomita 3 a karon farko a yankin Arewa maso Gabas.
Ya kuma kaddamar da titin kilomita ashirin wanda ya hada yankin Custom zuwa garejin Muna.

Shugaba Buhari ya kuma ziyarci makarantar tunawa da Tijjani Bolori inda kwamishinan ilimi Eng Abba Wakilbe ya tarbe shi tare da yin bayani.
Daga nan ya zarce zuwa fadar Shehun Borno inda suka gana da mai martaba sarki

A ziyarar da ya kai ta kwana daya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar cibiyar Distance Learning ta zamani a Jami’ar Maiduguri wanda Alhaji Muhammad Indimi ya gina kuma ya baiwa jami’ar tallafin.

Ya kuma bude, Makarantar Sakandare ta Tijani Bolori wadda Gwamnati ta gina a Kasheri.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara Maiduguri a watan Yunin bana inda ya kaddamar da ayyuka da dama a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply