Sheikh Dahiru Bauchi Ya Shawarci Al’ummar Musulmai Da Su Karbi Rigakafin Covid-19.

Babban malamin addinin musulunci sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga al’ummar musulmai da su karbi rigakafin cutar corona domin lafiyar su.

Yayi wannan jawabin ne yayin taron buda baki wanda wata kungiya mai zaman kanta ta shirya, malamin yace cutar corona gaskiya ne, inda ya bayyana cewa ya karbi rigakafin kuma yake shawartar jama’a da su karbi rigakafin.

Ya bayyana cutar corona a matsayin matsala ce ga duniya baki daya wanda kuma yake bukatar hadin kan kowa.

Haka kuma ya bukaci a’ummar musulmai da su rika amfani da takunkumin fuska, su wanke hannu da bin sauran ka’idoji da aka shimfida wajen kiyaye yaduwar cutar
Yayi alkawarin taimakawa tare da bada goyon baya a harkokin cutar a kowani yanayi domin kawo karshen sa a Najeriya dama duniya baki daya.

Haka kuma yayi magana kan cutar Lassa, sankarau, gudawa a sauran su kuma yayi kira ga hukumomin kiwon lafiya da ma’aikatan kiwon lafia da su cigaba da kokari wajen samun sakamako da ake bukata.

Anashi jawabin kodinetan jihar na kungiyar Journalists against Polio Alh. Lawal Dogara a yabawa babban malamin bisa kasancewa a yayi a sawun gaba wajen magana kan kiwon lafiya.