Shan Miyagun Kwayoyi Na Kawo Matsalar Huhu, Hanta Da Kuma Kwakwalwa

By: Juliet Bada, Maiduguri.

Majalisar dinkin duniya ta ware ko wace ranar 26 ga watan Juni na kowace shekara a matsayin ranar yaki da shan kwayoyi ta duniya.
Ofishin na majalisar dinkin duniya kan yaki da shan kwayoyi yana taimakawa gwamnati kan kalubalen da ake samu na masu shan maganin yadda suke yada manyan laifuka da ta’addanci tsakanin mutane.

Taken wan nan shekarar shine samun ilimin don kare kai akan shan kwayoyi da shigo dasu.Haka nan sun jaddada cewa akwai bukatar wayar wa da mutane kai kan matsalar magungunan da yadda suke kawo matsala, don haka ya kamata a wayarwa da mutane kai don kare lafiyarsu da kuma harkar tsaro.

San nan ofishin na karfafawa mutane da kungiyoyi gwiwa don su hada kai a wayar da kan mutane ta hanyar kafafaen sada zumunta na zamani.

A jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya da masu kula da harkar kwakwalwa sunyi kira ga gwamnati daga ko wane mataki dasu dinga wayar da kan mutane a kowane lokaci don kawo karshen matsaloli a yankin baki daya.

Wani likita a asibitin kwakwalwa na Maiduguri mai suna Sadiq Pindar yace an ware ranar ne don wayar da kan al’umma, wanda hakan zai sa a samu raguwar shan kwayoyin a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *