
Shahararran dan jaridar kasar amurka Larry King dake da shekaru 87 kuma yasha karban shaidar yabo ya kamu da cutar coronavirus wamda a yanzu yake karban kula a asibitin birnin Los Angeles na Amurka.
Kafar amurka da kuma iyalan sa sun shidar da cewa sama da sati daya kenan Larry na kwance a asibitin Cedars-Sinai Medical King,
Wata majiya ta shaidar da cewa Larry King a yan shekarunan yana fama da cututtuka ciki harda bugun zuciya, cutar suga da kuma cutar daji
Sa’annan biyu daga cikin ya’yansa 5 sun rasa ransu sanadiyyar cutar bugun zuciya daya kuma ciwon daji

A shekarar 1988 dan jaridar yayi kokarin samar da gidauniya wanda zai baiwa masu fama da matsalar zuciya marasa karfi damar biyan kudaden magani.
