Senator Ali Ndume Ya Umarci Lauyoyinsa Dasu Dakatar Da Tsayawar Da Yayiwa Abdulrasheed Maina.

alindume
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kwamitin sojoji a majalisar dattijai Senator Ali Ndume ya umarci lauyoyinsa dasu fara aikin dakatar da tsayawar da yayiwa tsohon shugaban kwamitin fansho Abdulrasheed Maina.

Ali Ndume wanda ke wakiltar kudancin Borno ya tsayawa Maina wanda ake kan shari’arsa a babbar kotun tarayya dake Abuja.

Mai shari’ar ya bukaci da sanatan ya kawo Maina duk inda yake tunda shi ya tsaya masa.

Senator Ali Ndume bayan tsayawa Mainan an bashi beli sai ya gudu ya bar kasar.
Alkalin ya garkame Ndume a gurin ajiye masu laifi dake Kuje bayan rashin ganin Maina yayin da ake cigaba da shari’a.

Ndume ya shiga tsaka mai wuya inda daga baya aka kama Maina a jmahuriyar Nijar.

A hirar sad a manema labarai Ndume ya yabawa shugaban yansanda na kasa Mohammed Adamu da sauran jami’an tsaro a kokarin da sukayi har aka kama Maina.

Haka nan ya godewa yan Najeriya baki daya musamman yan majalisar kasar, yan siyasa day an uwa da abokan arziki .

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply