Sarkin musulmi Yayi Alhinin Rasuwar AbdulAzeez Ude

Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya bayyana rashin dadinsa game da rasuwar AbdulAzeez Ude.

cikin sanarwa da mataimakin san a harkar labarai Bashir Adefaka ya fitar, sarkin musulmin yace marigayin ya kasance mai gogomarya ga jama’a musamman ma ga al’umman musulmi wanda al’umma zasuji radadin rashin sa.

Sanarwar na kunshe da cewa, yayi jimamin rashin marigayi Ude wanda da dadewa tun lokacin da yayi aiki da rundunar sojin Najeriysa a yankin gabashin Najeriya.

Sannan kafin rasuwar sa shine shugaban wallafe-wallafe na mujallar Newswatch kuma yace hakika yan Najeriya sunyi rashin sa.

Haka nan Sultan din yayi addu’ar Allah ya gafarta masa yasa shi a Al-Jannat Firdaus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *