Sarkin Musulmi Ya Yawo Ziyara Jihar Borno

borno state small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sarkin musulmi kuma shugaban sarakunan gargajiya na kasa Sa’ad Abubakar yace yanayin tsaron kasar ya munana kuma ya bukaci rundunar soji dasu kewaye dajin sambisa da kuma yankin tapkin chadi da yan Boko Haram ke fakewa ciki.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin ta’aziya da yakawo wa gwamnan jihar borno da kuma jama’a jihar Borno duka game da kashe manoma da yan kungiyar na Boko Harma sukayi a filin nomar shinkafa a Zabarmari.

Haka zalika Sultan Abubakar yace sun iso Maiduguri ne ba domin yin jaje ga gwamnan ba kadai harma da bayani game da rashin tsaron daya addabi kasar.

Yace yan ta’adda da kuma yan bindiga na ko ina a yankin na arewa maso gabas .

wanda ya takura rayukan jama’a kuma hakan ma a kudancin kasar wanda yace kasha-kashen ya dauki sabon salo kuma babu wanda yasan dalilin kisan raayukan da basuji ba basu gani ba da akeyi.

Yace ya dauki matakin isowa da sunan majalisar sarakunan kasar kuma yayi furucin ba ga gwamna zulum kadai ba sai de ga dukkan gwamnoni kasar , yayi musu kira cewa a hadu gaba daya domin magance matsalolin karkashen rayukan jama’a da akeyi.

Ana shi bangare gwamna Zulum ya godewa majalisar sarakunan bias ziyarar kuma ya koka game da yadda akaci gaba da dogaro da tallafi wajen ciyar da yan gudun hijira

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply