Sanata Shekarau Yayi Allah Wadai Da kisan Gillar Da Akayi A Kauyen Zabarmari .

ibrahim-shekarau
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sanata Ibrahim Shekarau dake wakiltar mazabar Kano ta arewa ya jajantawa gwamna da daukacin jama’ar jihar nan kan kisan gillar da yan ta’addan BH suka yiwa manoma a Zabarmari.

Yace amadadin al’ummar mazabar sa, yayi Allah wadai da kisan da aka yiwa manoman wanda yayi sandaiyar rayukan jama’a marasa karfi a cikin al’umma.

Yayi addu’an Allah ya jikan wadan da suka rasa rayukan su da rahama kuma ya sa aljanna ce makomar su.

Haka kuma yayi addu’ar Allah ya baiwa wadanda suka rasa yan uwan su juriyar rashi.

Daga karshe yayi kira ga al’umma baki daya da su maida hankali kan yanayin tsaro kuma su hada hannu da gwamnati da hukumomin tsaro domin kare kai baki daya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply