Sanata Kashim Shettima Ya Mika Ta’aziyar Sa Ga Jama’an Jihar Borno Bisa Rashin Sarkin Dikwa

kashim
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Tsohon gwamnan jihar sanata Kashim Shettima ya mika ta’aziyar sa ga jama’an jihar Borno bisa rashin sarkin Dikwa mai martaba Shehu Muhammad ibn Abba Masta na biyu. 

Sanatan ya wallafa a shafin sa na Facebook tare da yaba marigayin a matsayin gwarzo kuma daya daga cikin wadanda suka kai ilimi gaba a yankin.
Yace marigayi Shehu Muhammad tauraro ne na zaman lafiya, da kyautatawa wanda salon shugabancin sa ya zama abin koyi ga jihar Borno da Najeriya baki daya.

Ya mika ta’aziyar sa ga iyalan marigayin da masarautar Dikwa, da kuma jama’a da gwamnatin jihar Borno tare da addu’ar Aljannan a gare shi

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply