Sadiya Farouq Ta Yi Allah Wadai Da Kashe-Kashe Da Lalata Dukiyoyi A Kudancin Borno Da Adamawa.

sadiya umar faruk
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Chimezie Godfrey
Ministar kula da ayyukan jin kai, da walwalar jamaa, Sadiya Umar Farouq, ta yi Allah wadai da kashe-kashe da lalata dukiyoyi a Kudancin jihohin Borno da Adamawa.

A wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakatare na Maaikatar, Bashir Nura Alkali, Ministan wanda ta nuna damuwa game da harin da aka kai Pemi, dake karamar Hukumar Chibok, da wasu garuruwa hudu da ke karamar Hukumar Hawul a Kudancin Borno da Garkida a Jihar Adamawa. inda ta baiyana harin a matsayin Rashin imanin.

Ta ce, abin takaici ne ace wadannan hare-haren ta’addanci sun na faru a lokacin da mutane suke cikin jin dadin hutun Kirsimeti tare da ‘yan uwansu.
Ministan ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da hare-haren sannan kuma ta yabawa hukumomin da abin ya shafa da kuma Gwamnan, Babagana Zulum da ziyarar da yakai yankin .

A karshe Ta bayyana cewa ana shirye-shiryen tura kayan agaji ga wadanda harin ya shafa

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply