Sabon Babban Hafsan Sojojin Kasa Manjo Janar Ibrahim Attahiru Ya Kama Aiki,

FB_IMG_1611683617823
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sabon babban hafsan sojojin kasa manjo janar Ibrahim Attahiru ya kama aiki, bayan an tsige sa daga kwamandan shirin operation Lafiya Dole da tsohon hafsan sojoji laftanar janar TY Buratai yayi sakamakon zargin sa da akayi na kisan gillar da akayiwa mutane dari 1 da 40 a jihohin Delta da Anambra.

An nada manjo janar Attahiru a matsayin babban hafsan sojojin kasa tare da sauran hafsoshin tsaro a ranar Talata.

Manjo janar Attahiru wanda yam aye gurbin Irabo a matsayin kwamandan shirin operation Lafiya Dole a shekarar 2017 wanda Buratai ya tsige bayan nasarorin da yan ta’adda suka samu akan sojoji karkashin shugabancin sa musamman a Maiduguri.

Buratai ya bashi umurnin ya kama shugaban Boko Haram da rai ko a mace cikin kwana 40, wanda hakan baiyi ba kuma yayi sanadin samun nasarori gayan Boko Haram akan sojoji wanda hakan ya sa aka zarge sa da kisan gillar da yayi sanadiyan mutuwar mutane sama da dari 1 da 40 a lokacin da yake mukaddashin kwamanda na shiyya na 82 a shekarar 2015.

Manjo janar Attahiru wanda ya fito daga yankin karamar hukumar Kaduna ta arewa a jihar Kaduna kuma ya kasance mamba a makarantar tsaro na kasa na karo 35.

An samu nasarori karkashin shugabancin sa a bangarori da dama a rundunar sojojin Najeriya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply