Sabbin hafsoshin sojoji sun kawo ziyarar farko zuwa Maiduguri domin ganawa da gwamna Zulum.

FB_IMG_1612177193312
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil Ngala and Ali Muhammed Zanna,

Hafsoshin tsaron Najeriya sun kawo ziyarar farko zuwa jihar Borno wanda ya kasance cibiyar da yan kungiyar Boko Haram ke kawo hari inda suka gana da gwamna Babagan Umara Zulum tare da sanata Kashim Shettima.

Shugaban ma’aikatan tsaro manjo janar Leo Irabor ne ya jagoranci tawagar hafsan sojojin kasa, manjo janar Ibrahim Attahiru, hafsan sojan ruwa,Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo sai kuma hafsan sojojin sama Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao zuwa gidan gwamnatin anan Maiduguri.

Yayin da yake jawabi ga hafsoshin sojojin, gwamna Zulum yayi kira a gare su da su hada kai da jami’an kasashen Chadi, Kamaru da kuma Nijar.

Gwamna Zulum ya cigaba da cewa ya kamata a hada kai da jami’an da fararen hula domin samun uarda da kuma dama wajen tattara bayanan sirri wanda ya bayyana hakan dacewa shine hanyar nasara wajen yaki da yan ta’adda.

Ya tabbatar musu da manufar gwamnatin sa na taimaka musu wajen yaki da yan ta’adda, kuma yayi kira a garesu da su kasance masu aiki da adalci da gaskiya domin samun cigaba.

Ya kara dacewa domin samun nasara, dole a samu kyakkyawan alaka tsakanin hukumomin tsaro musamman ma jami’an sojojin sama dana kasa.

Jagoran tawagar, shugaban ma’aikatan tsaro manjo janar Leo Irabor ya tabbatar da cewa jami’an sojoji zasuyi iya kokarin su wajen kawar da yan ta’adda baki daya, kuma ya bukaci hadin kai daga fararen hula wajen yakar yan ta’adda.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply