Rundunar Yansandan Najeriya Sun Gayyaci Bukola Saraki

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar Yansandan Najeriya sun kirayi shugaban majalisar datttijai Bukola Saraki don amsa zargin da ake masa na alaka da mutanen da suka kai hari Bankuna a garin Offa dake jihar Kwara a watan Afirilu.

Mutane 5 daga cikin 15 da ake zargi da aka kama sun bayyana sunansa a cikin bayanan su. Saraki ya karyata zargin ta bakin mai Magana da yawunsa Yusuf Olaniyonu yace idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ya fada wa takwarorinsa labarin daya samu daga gwamnan jiharsa Dr. Abdulfatah Ahmed kan cewa shugaban yansandan na kasa Ibrahim Idris kan yana so ya danganta shi da masu tsafi da aka kama a jiharsa ta Ilorin.

Ya kara da cewa anyi haka ne don a tozarta shi don sunyita gayyatar shugaban yansandan ne yaki amsa gayyyatar tasu.

Yace a matsayinsa na dan kasa mai bin doka yana jira su aika masa takardar gayyata ta hanyar da ya kamata, shi kuma zaije.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply