Rundunar Yan Sandan Jihar Gombe Ta Kama Shahararren Mai Garkuwa Da Yara

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yansandan jihar Gombe ta kama shahararren mai garkuwa da yara inda ta maid a wasu yara da ba’a samu iyayensu ba jihar Anambra.

Idan za’a iya tunawa ranar 22/10/2019 bayan binciken sirri da yansanda suka gudanar da hadin gwiwar rundunar yansandan na jihar Anambra sun kama mata da ake zargi da safarar mutane a Unguwar Nkpor Market a titin Tarzan Junction dake karamar hukumar Idemili ta arewa dake jihar ta Anambra da yara 3 da suka sato.

Bincike ya bayyana cewa yaran an sato su daga jihar Gombe wanda wata mai suna Hauwa Usman ta sato ta kaisu jihar Anambra ranar 20/10/2019.

Bayan sanarwar da rundunar yansandan tayi ranar 27/10/2019 wasu iyaye biyu daga jihar Gombe sunje Awka inda suka gane yaransu guda 3, inda tuni yaran 3 suka hadu da iyayensu kuma aka mika wadanda ake zargin zuwa sashin bincike don yanke musu hukunci.

Haka nan yayin bincikenda rundunar yansandan jihar Gombe suke wadanda ake zargin sun bayyana cewa suna sato yaran su sayarwa wata mata mai suna Mrs Nkechi Odinye dake Anambra wadda take siyan yaran kan kudi daga dubu dari biyu zuwa dubu dari hudu ya fdanganta da shekarunsu da kuma jinsi.

Haka nan kwamishinan yansandan John B Abang ya bukaci jama’a dasu yada bayanin kuma duk wanda yake da wani cikakken bayani ya tuntubi jami’in yada labarai da hulda da jama’a ko wan nan lambar wayar 08060970639.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply