Rundunar Yan Sandan Jihar Adamawa Sun Fara Bincike Zarge Cewar Za’a Hada Sasun Tsiraici A Jihar

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yan sandan jihar Adamawa sun fara bincike a game da zarge-zarge na cewar za’a hada chasun nuna tsiraici a wani boyeyyen waje a ranar goma ga watan janairu a cikin jihar

Gidan Radiyo Dandal, Kura Radio tace ta gano cewar akwai shiri da akeyi na mussanman domin hada wannan casun.

Tace anyi niyar hada chasun amma jami’an yan sanda sun shiga al’amarin domin hanawa.

Tallan chasun da za’a yi a gabar teku a yola ya karade garine a kafofin yada labarai ta zamani a cikin sattanni da suka gabata inda ake bayyana cewa za’a biya kudi naira dubu biyu kafun a shiga.

Da jin hakkan ne mai Magana da yawun rundunar DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya bayyana cewa Kwamishinnan yan sandan jihar bada umarnin yin bincike akan al’amarin.

A wani labari mai kama da hakkan kuma a jihar kaduna an samu labarin cewa ana zargin wasu da hada irin wannan chasun inda tuni yan sanda sukayi bincike tare da kama wadan da ake zargin.

Inda Gwamnnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada umarnin rusa filin chasun wanda hakkan ya jawo cece-ku ce domin wace ta mallaki wurin ta mussanta shirin da akeyi na shirya wannan chasun a wurin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply