Rundunar Yan Sanda Jihar Bauchi Ta Kama Mutane 20 Da Take Zargi Da Shirya Taro Na lalata.

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yan sandar jihar BAUCHI ta kama mutane 20 da take zargi da shirya taro na lalata.

Yayin gabatar damasu laifin a hedikwatan rundunar jihar, kwamishinan yan sandar jihar Lawal Tanko Jimeta yace an kamasu bayan samu sahihinn bayanin abinda sukeyi.

Dayake jawabi, jami’I mai hulda da jama’a DSP Ahmed Wakili daya wakilci kwamishiinan, yace sun samu labarin takurawa jama’a da yan daba na Sara-Suka keyi, sace-sace da sauran ayyukan bata gari.

Abubuwan da aka gano daga wajensu sun hada da wukake 3, adda 1, da sauran su.
Masu laifin sun hada da Ishaya Adamu mai shekaru 19 sai Mohammed Abdullahi Lawwali shekara 22,Ayuba Adamu shekara 19, da Aminu Tago shekara 19, sai Mubarak Baba mai shekaru 22 da sauran su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply