Rundunar sojojin saman Najeriya tace zata dauki wadanda suka kammala makarantar sakandare cikakken aikin sojan sama.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar Sojin saman Najeriya ta sake gabatar da shirin wadanda suka kammala karatun sakandare, wanda aka fi sani da Ex-Junior Airmen cikin aikin soja a matsayin sojan sama.

Babban hafsan sojojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, ne ya sanar da hakan a yayin fareti na 36 na kammalawar ƙananan sojojin sama na makarantar sojojin sama da ke Jos a Jihar Filato.

Amao wanda Air Vice Marshall Isa Muhammad ya wakilta, ya ce wasu daga cikin ɗaliban da suka nuna sha’awarsu ta hidimtawa ƙasarsu sun shiga cikin shirin kuma an tura su zuwa rundunonin sojin zaman daban -daban a duk faɗin Najeriya bayan sun sami horo na ƙarfafawa a cibiyar horar da sojoji dake Kaduna.

Ya ce, “Matsayin horon da kuka samu yayin da kuke makarantar sojojin sama ba zai zama da amfani ba idan bakuyi amfani da wannan yunƙurin daidai gwargwado na hidima ga kasar mu a matsayin sojan sama.

Babban hafsan sojin ya kuma yi kira ga wadanda suka kammala karatun su dasu cigaba da kiyaye kyawawan dabi’un da suka koya yayin da suke makarantar sakandare da wadanda za su koya a cikin hidimar, don ba su damar kiyaye manyan matakan da rundunar ke sa ran su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply