Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Amince Da Canjin Wuraren Aiki Ga Manyan Dakarun Ta.

troop3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban hafsan rundunar sojojin kasa laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da sabbin canjin ayyuka da wajen aiki ga wasu manyan ofisoshi zuwa wurare daban daban domin sabunta kwarewar su.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar birgediya janar Sagir Musa shi ya bayyana haka a wata sanarwa a Abuja, yace canjin ayyuka wajen aiki, aiki ne na yau da kullum domin karfafa tsarin wajen cigaba.

Canjin ayyuka da wajajen aikin ya fara da manjo janar F O Agugo daga shalkwatan bangaren sigina dake Apapa a jihar Legas zuwa shalkwatan tsaro a matsayin shugaban sadarwa na tsaro.

Haka kuma manjo janar M Muhammad wanda yake cibiyar kayaki na rundunar a Abuja yanzu ya koma Pronto Tech Nigeria Limited a matsayin manajan darakta, sai kuma manjo janar A R Owolabi daga shalkwatan tsaro zuwa sashin sadarwa a shalkwatan sigina na rundunar a matsayin kwamanda.

Sauran akwai manjo janar Hussein Ahmed a matsayin shugaban marshal da kuma manjo janar Abdul Khalifa Ibrahim a matsayin kwamandan shiyya na 7 da operation lafiya dole shiyya na 1 a Maiduguri.

Sanarwar ta kara dacewa sukkan wadanda aka canza su zasu fara aiki daga ranar 18 ga wannan watan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply