Rundunar Sojojin Najeriya Zasu Gudanar da “Operation Last Hold”

nigerian_nigeria_army_soldiers_military_combat_field_uniforms_007
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin najeriya zasu gudanar da hare-haren karshe mai suna “Operation Last Hold” a yammacin  Borno da yankin kogin tafkin chadi don dawo da walwala da tatalin arziki a yankin, hade da maida yan gudun hijira matsugunan su.

Shugaban kula da horo da ayyuka na rundunar Maj.-Gen. David Ahmad ne ya bayyana hakan ranar juma’a a taron manema labarai.

Ahmadu yace za’a fara gudanarwa ranar 1 ga watan Mayu kuma zai kai wata 4 don a samu a gyara yankin na tafkin Chadi da hanyar ruwa da kuma duk abinda zai hana jiragen ruwa da mutane aiki a yakin.

Don kuma a tabbatar da an kawo karshen guraren da yan Boko haram suke zama a yankin na tafkin Chadi. Da kuma ceto wadanda ke hannun yan kungiyar ta boko haram din.

Kuma suna sa ran wan nan shine karo na karshe da za’a samu nasara a kan kungiyar ta Boko Haram, wanda hakan zai ba masu kamun kifi da wasu ayyyukan da ke kawo tattalin arziki a yankin. Kuma hakan zai bada damar maida yan gudun hijira gidajensu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply