
Rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole ta kawar da yan ta’adda tare da lalata mabuyar su a dajin Sambisa wanda kuma take zargin sune suka kai haren-hare a kudancin jihar Borno da Adamawa cikin kwanakin nan.
Shugaban sashen al’amuran labaru na hedikwatan tsaron kasar manjo janar John Enenche ne ya bayyana hakan.
Manjo Enenche yace ayyukan da rundunar saman ke gudanarwa hakika yayi karya logon yan ta’addan a yankin arewacin kasar tare da cewa ko a ranar 28 ga watan disamban wannan shekara sun yi luguden wuta a dajin Sambisadake jihar Borno.

Ya kuma ce sun kai samaman ne bayan samun bayan tattara bayanai tare da gano yankin day an ta’adda da sukayi barnar a kudancin Bornon da arewacin Adamawa ke mafaka.
Yace cikin samaman da rundunar takai, sunyi nasarar lalata mafakar su harma da wasu makamai tare kuma da kashe da dama daga cikin su.
