Rundunar sojojin Najeriya sun sauya sunan shirin yakin da suke da yan ta’adda.

Rundunar sojojin Najeriya ta sake fasalin aikin ta na yaki da yan ta’adda a yankin arewa maso gabas.

Rundunar ta sauya sunan shirin na ta a yankin arewa maso gabas daga shirin Operation Lafiya dole zuwa operation Hadin kai wanda aka tsara don nuna sabon yanayin aikin hadin guiwar sojoji.

Rundunar ta bayyana haka a ranar Juma’a, cewa hafsan sojojin Najeriya ne ya amince da hakan.

Mai Magana da yawun rundunar yace an tsara hakan ne kan cewa sojojin sun samu nasarori da dama a tsawon shekaru kuma suna bukatar daidaitawa don ingantaccen aiki.

Jerin sauye sauyen da akayi na daga sauye sauyen cikin gida da sabbin hafsoshin sojin sukayi don bunkasa hadin kai da hade kan ayyuka kan yan ta’adda.