Rundunar Sojojin Najeriya Sun Musa Rahotan Dake Cewa Yan Boko Haram Sun Kashe Sojojin 20.

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin najeriya sun musa rahotan cewar sojoji 20 ‘yan boko haram da Islamic state west african province suka kashe a arewa maso gabas.

Daraktan yada labarai na sojin, Brig.-Gen. Mohammad Yerima ne ya bayyana hakan ranar alhamis a babban birnin tarraya abuja cewa labaran ba gaskiya bane.

Yerima yace an bayyana rahotan ne domin tayarwa da al’umma hankali da kuma nuna gazawar dakarun sojojin dukda jajircewar su wajen yakar ‘yan ta’addan.

Ya kara da cewa babu harin da’aka kai har aka kashe sojoji 20.

Yerima yace, harin da ‘yan ta’addan suka kai kan hanyar da’akeyi dakuma geidam, rundunar ta mobile strike team da bataliya ta rundunar 159 sunyi maganin ‘yan ta’addan.

Ya kara dacewa, sojojin sunyi sadaukarwa sosai inda biyu daga cikin su suka samu raunuka kuma suke asibiti a halin yanzu.
A bayaninsa, yace kungiyar ‘yan ta’addan na boko haram da ISWAP suna cikin mawuyacin hali na neman abinci, magunguna, da sauran kayyayaki a halin yanzu da rundunar operation Tura Takai Bango suka kai samame sansanin su.

Yayi kira da mutane kan su cigaba da bawa jami’an tsaro hadin kai don yakar ‘yan ta’addan a kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply